2 Timothy 4

1A gaban Allah da kuma Kiristi Yesu, wanda zai yi wa masu rai da matattu shariʼa, saboda kuma bayyanuwarsa da mulkinsa, ina ba ka umarni: 2Ka yi waʼazin Maganar Allah, ka zama a shirye a kullum, ko da zarafi, ko babu zarafi, ka yi gyara, ka kwaɓe, ka kuma ƙarfafa-da matuƙar haƙuri da koyarwa cikin natsuwa. 3Gama lokaci yana zuwa da mutane ba za su jure da sahihiyar koyarwa ba. A maimako, don cimma burinsu, za su taro wa kansu malamai masu yawa, domin su faɗi abin da kunnuwansu masu ƙaiƙayi suke so su ji. 4Za su juye kunnuwansu daga gaskiya zuwa ga jin tatsuniyoyi. 5Amma kai, ka kame kanka ta kowane hali, ka jure shan wahala, ka yi aikin mai bishara, ka cika dukan ayyukan hidimarka.

6Gama an riga an tsiyaye ni kamar hadaya ta sha, kuma lokacin tashina ya yi. 7Na yi fama mai kyau, na gama tseren, na riƙe bangaskiya. 8Yanzu kuwa an ajiye mini rawanin adalci, wanda Ubangiji, Alƙali mai adalci zai ba ni a ranan nan-ba kuwa ni kaɗai ba, amma ga duk waɗanda suka yi marmarin bayyanuwarsa.

Maganar Ƙarshe

9Ka yi iyakacin ƙoƙarinka ka zo wurina da sauri, 10gama Demas, saboda ƙaunar wannan duniya, ya yashe ni ya tafi Tassalonika. Kirskens ya tafi Galatiya, Titus kuwa ya tafi Dalmatiya. 11Luka ne kaɗai yake tare da ni. Ka nemi Markus ku zo tare, domin yana da amfani a gare ni cikin hudimata. 12Na aiki Tikikus zuwa Afisa. 13Saʼad da za ka dawo, ka zo mini da alkyabbar da na bari a wurin Karbus a Toruwas, da kuma naɗaɗɗun littattafaina, tun ba ma fatun nan masu rubutu ba.

14Alekzanda maƙerin ƙarafan nan ya yi mini mugunta ƙwarai. Ubangiji zai sāka masa saboda abin da ya yi. 15Kai ma sai ka lura da shi, domin ya yi gāba sosai da saƙonmu.

16A lokacin da na kāre kaina da farko, ba wanda ya goyi bayana, sai ma kowa ya yashe ni. Ina fata ba za a lasafta wannan laifi a kansu ba. 17Amma Ubangiji ya tsaya tare da ni, ya kuma ba ni ƙarfi, don ta wurina a yi cikakkiyar shelar saƙon har Alʼummai duka su ji. Aka kuma cece ni daga bakin zaki. 18Ubangiji zai cece ni daga kowane mugun hari yǎ kuma kai ni mulkinsa na sama lafiya. A gare shi ɗaukaka ta tabbata har abada abadin. Amin.

Gaisuwa ta Ƙarshe

19Ka gai da Firiskila da Akwila da iyalin Onesiforus. 20Erastus ya dakata a Korinti, na kuma bar Turofimus cikin rashin lafiya a Melitus. 21Ka yi iyakacin ƙoƙarinka ka iso nan kafin damina. Yubulus yana gaishe ka, haka ma Fuden, Lainus, Kalaudiya da kuma dukan ʼyanʼuwa.

22Ubangiji yǎ zama tare da ruhunka. Alheri yǎ zama tare da ku.

Copyright information for HauSRK